• Home  
  • Kotu ta wanke Abba Kyari kan zargin rashin bayyana kadadrori
- Babban Labari - Labarai

Kotu ta wanke Abba Kyari kan zargin rashin bayyana kadadrori

Babbar kotun tarayyar Najeriya ta sallami dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yansanda Abba Kyari, ta kuma wanke shi daga wasu zarge-zargen da ake masa. Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin kan zarge-zarge 23 da ake masa da suka shafi rashin bayyana kadarorinsa da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar (NDLEA) ta shigar […]

Babbar kotun tarayyar Najeriya ta sallami dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yansanda Abba Kyari, ta kuma wanke shi daga wasu zarge-zargen da ake masa.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin kan zarge-zarge 23 da ake masa da suka shafi rashin bayyana kadarorinsa da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar (NDLEA) ta shigar a kan sa.

An gurfanar da DCP Abba Kyari tare da wasu ‘yan’uwansa biyu, waɗanda ake zargin su da yin rantsuwar ƙarya domin yin rufa-rufa wajen ɓoye asalin mamallakin dukiyar.

A yayin yanke hukuncin, mai shari’a Omotosho ya ce NDLEA ya kasa gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da zargin da ake yi masa.

Alƙalin ya bayyana cewa ana iya mallakar fili ta hanyar gado ko kyauta da sauran su.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000