Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya zargi jam’iyyun adawa da karkatar da bayanai kan Dokar Zabe ta 2026 domin amfanin siyasa. Ya ce dokar ta fito ne ta hanyar sahihin tsarin majalisa da sauraron ra’ayoyin jama’a, don haka suka da ake yi mata na iya kawo illa ga dimokuradiyya.
Ya kuma musanta zargin cewa APC na kokarin mayar da Nijeriya kasa mai jam’iyya daya, yana mai cewa dimokuradiyya na bukatar adawa mai karfi domin inganta shugabanci. Tinubu ya ce yawaitar sauya sheka zuwa APC alama ce ta amincewar jama’a da manufofin jam’iyyar.
Shugaban ya gargadi ‘yan APC da su guji rikicin cikin gida, yana mai cewa hadin kai shi ne ginshikin nasara. Ya kuma kare sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, yana cewa duk da wahalhalu, sun fara haifar da sakamako mai kyau ga tattalin arzikin kasa.

