• Home  
  • Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya ƙara naira tiriliyan 9 cikin kasafin kuɗin 2026
- Babban Labari

Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya ƙara naira tiriliyan 9 cikin kasafin kuɗin 2026

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi Majalisar Dokokin Ƙasa ta amince da ƙara naira tiriliyan 9 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda hakan zai ɗaga jimillar kasafin daga naira tiriliyan 58.4 zuwa naira tiriliyan 67.4. An bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisa […]

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi Majalisar Dokokin Ƙasa ta amince da ƙara naira tiriliyan 9 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda hakan zai ɗaga jimillar kasafin daga naira tiriliyan 58.4 zuwa naira tiriliyan 67.4.

An bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisa na ranar Talata.

Shugaban ya bayyana cewa wannan ƙarin na da nufin buƙasa fayyace kashe kuɗaɗe da kuma aiwatar da wasu manyan tsare-tsaren gwamnati.

A cewarsa, ƙarin zai taimaka wajen ƙarfafa tsarin kasafin kuɗi da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya ce akwai muhimman dalilai uku da suka sa aka nemi wannan ƙarin.

Daya daga cikinsu shi ne buƙatar daidaita da kuma biyan wasu haƙƙoƙi na shari’a da suka rage daga tsofaffin kasafin kuɗi, domin kada su hana aiwatar da kasafin shekarar 2026 yadda ya dace.

Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen samun cikakken tsari na kuɗin gwamnati da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da su cikin gaskiya da inganci.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai