• Home  
  • An kama mutum 2 kan zargin sayar da filayen gwamnatin a Kano
- Labarai

An kama mutum 2 kan zargin sayar da filayen gwamnatin a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta kama wasu mutum biyu bisa zargin rabawa da sayar da filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba a yankin Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo. Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane na jihar, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce […]

Gwamnatin Jihar Kano ta kama wasu mutum biyu bisa zargin rabawa da sayar da filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba a yankin Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo.

Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane na jihar, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce waɗanda aka kama na daga cikin mutanen da ake zargi da mamaye filayen gwamnati tare da sayar da su ba bisa ka’ida ba.

A cewarsa, bayan matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin kawo ƙarshen rikicin filaye a Rimin Zakara, waɗanda ake zargin sun koma yankin Gundutse da ke Karamar Hukumar Kura, inda suka ci gaba da gudanar da haramtattun hada-hadar filaye.

Kwamishinan ya bayyana sunayen wadanda aka kama da Muhammad Kabir, mai shekaru 57 daga unguwar Gaida, da Kamilu Iliyasu, mai shekaru 55 daga yankin Zoo Road.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da neman wani da ake zargi mai suna Mustapha Matazu, wanda ake kyautata zaton ya tsere.

Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya yi Allah wadai da ci gaba da mamayewa da sayar da filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamo tare da gurfanar da duk masu hannu a irin waɗannan ayyuka.

Ya kuma shawarci jama’a da su riƙa tabbatar da sahihancin mallakar duk wani fili kafin su saya ta hanyar tuntuɓar Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane ta jihar, yana mai gargaɗin cewa yin hakan zai taimaka musu wajen kauce wa faɗawa hannun masu damfara.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai