Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Haruna A. Yahaya, ya kai ziyara cibiyoyin rubuta jarrabawar JAMB, don duba yanayin tsaron wuraren da ake gudanar jarrabawar.
Ziyarar tasa na da nufin tabbatar da cewa an gudanar da jarrabawar cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma bin tsari, ba tare da an samu wata matsala ba.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Lawan Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar asabar.
Sanarwar ta ce kwamishinan ƴan sandan ya yaba da yadda jami’an tsaron ke gudanar da aikin bayar da tsaro, ya tabbatar da cewa duk wanda yayi yunkurin tayar da hankalin al’umma ba za a saurara masa ba.
A ƙarshe rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa a shirye wajen ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.
