Rundunar yan sandan jihar Kano, karkashin jagorancin kwamishina, CP Ibrahim Adamu Bakori, ta kammala horas da jami’ai 200 kan dabarun sarrafa makami domin ƙara musu ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan tsaro.
Horon na tsawon wata guda, wanda aka gudanar a sansanonin rundunar yan sandan kwantar da tarzoma ta lamba 9 da ke Hotoro da ta 52 da ke Challawa, ya shafi dabarun tunkarar masu aikata laifuka da yadda za a yi amfani da makami da kuma bin ƙa’idojin aikin yan sanda.
Da yake jawabi a wajen bikin kammala horon, mukaddashin kwamishinan yan sandan Kano, DCP Audu Sabo, ya ce rundunar ta himmatu wajen samar da jami’ai masu ƙwarewa da hazaka da kuma mutunta haƙƙin jama’a.
Ya bayyana cewa jami’an sun samu horo kan mutuntata haƙƙin ɗan Adam da yin aikin tsaro tare da jama’a.
DCP Sabo ya buƙaci jami’an da suka kammala samun horon su yi amfani da dabarun da suka samu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da ƙwarewa.
Rundunar yan sandan Kano ta ce za ta ci gaba da horas da jami’anta domin ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
