Hukumar tsaron civil defence NSCDC reshen jihar Kano, ta kama mutane uku da ake zargi da satar wayoyin lantarki da kuma babur mai kafa uku.
Cikin wadanda jami’an hukumar suka kama sun hada da , Adamu Ibrahim da Abba Ado, wadanda ake zarginsu da lalata wayoyin lantarki da kuma sata, masu tsawon mita 300 a ƙauyen Yunfawa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Kano.
Haka zalika hukumar ta kama, wani mai suna, Abdullahi Aminu mai shekaru 18 da ake zargin ya sace babur mai kafa uku dauke da wata mata a ciki a yankin Kofar Waika zuwa Kofar Dawanau.
Kakakin NSCDC, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana cewa wadanda ake zargin suna tsare a hannunta don gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Suma waɗanda ake zargin sun bayyana cewa lokacin da suke yanko wayar jami’an tsaron suka kama su.
