Jami’an hukumar kwastam biyu sun rasa ransu a fafatawar da suka yi da mayaƙan da ake zargi Lakurawa ne a jihar Kebbi.
Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an masu muƙamin ASC da DSC, sun rasa ransu ne yayin samamen yaƙi da ƴan ta’adda da tsakiyar dare.
Adeniyi ya faɗi hakan ne a birnin Illorin yayin da yake gabatar da jawabi a jami’ar Illorin da ke jihar Kwara.
Rahotanni sun ce maharan sun farwa shingen binciken ababen hawa na tsaro da ke kusa da juna.
A nan ne kuma suka harbi jami’i guda sannan suka cinna wa ɗaya jami’in wuta da ransa.
Gwamnan jihar Kwara, AbdurRahman AbdulRazaq ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga hukumar ta kwastam kan mutuwar jami’an biyu inda ya bayyana su a matsayin ƴan kishin ƙasa da suka rasa ransu yayin hidimta wa ƙasarsu.
