• Home  
  • Tsohon Shugaban ’Yan Sanda ya janye daga takarar Gwamnan Yobe
- Babban Labari - Siyasa

Tsohon Shugaban ’Yan Sanda ya janye daga takarar Gwamnan Yobe

Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alƙali, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar Gwamnan Jihar Yobe. Usman Baba Alƙali wanda ke neman takarar Gwamnan Yobe a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC, ya sanar da haka ne ta wata takardar sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ya bayyana cewa ya yanke shawarar janyewa ne […]

Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alƙali, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar Gwamnan Jihar Yobe.

Usman Baba Alƙali wanda ke neman takarar Gwamnan Yobe a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC, ya sanar da haka ne ta wata takardar sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa ya yanke shawarar janyewa ne domin tabbatar da samun haɗin kai da daidaito da kuma nasarar APC da kuma ci-gaban Jihar Yobe.

A cewarsa ya ɗauki matakin ne bayan ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum da kuma Gwamna Mai Mala Buni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar  APC a ƙananan hukumomi 17 na Jihar Yobe.

Don haka ya roƙi magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu tare da mara baya ga duk wanda ya zama ɗan takarar gwamna a jam’iyyar.

Kafin nan, tsohon Shugaban ’yan sandan yana daga cikin mutane shida masu neman takarar a jam’iyyar, kuma  ya dage a kan cewa dole sai jam’iyyar ta yi zaɓen fid-da-gwani maimakon sasanta ’yan takarar.

Hakan ta faru ne bayan shi da wasu takwarorinsa sun yi watsi da zaɓin Baba Malam Wali da Gwamna Mai Mala Buni da Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Ibrahim Geidam da wasu masu ruwa da tsaki suka yi a matsayin ɗan takarar sasanci.

Sauran waɗanda suka yi watsi da zaɓin Baba Malam Wali su ne, Ibrahim Bomai, Mustapha Maihaja, Bashir Machina, Kashim Musa Tumsah. Lawan Kolo Geidam janye tare da goyon bayan dan takarar da shugabannin jam’iyyar suka zaɓa.

Yanzu da janyewar Usman Baba, yawan masu neman takarar Gwamnan Jihar Yobe a Jam’iyyar APC ya koma huɗu ke nan—Sanata Ibrahim Bomai, Mustapha Maihaja, Bashir Machina da kuma Kashim Musa Tumsah.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000