• Home  
  • Ɗan Ganduje Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Majalisar Tarayya A NDC
- Babban Labari

Ɗan Ganduje Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Majalisar Tarayya A NDC

Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayi fom ɗin takarar kujerar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC. Zai tsaya takarar ne a mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado da ke Jihar Kano. Duk da kasancewar mahaifinsa a jam’iyyar APC, Abdulaziz, ya daɗe yana bin siyasar Kwankwasiyya kuma yana […]

Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayi fom ɗin takarar kujerar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.

Zai tsaya takarar ne a mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado da ke Jihar Kano.

Duk da kasancewar mahaifinsa a jam’iyyar APC, Abdulaziz, ya daɗe yana bin siyasar Kwankwasiyya kuma yana da kusanci da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, ya nuna Abdulaziz yana ganawa da Kwankwaso jim kaɗan bayan ya sayi fom ɗin takararsa, inda aka ce ya yi masa bayani kan burinsa na shiga takara kafin babban zaɓe mai zuwa.

Wannan lamari na nuna irin yadda siyasa ke gudana tsakanin Ganduje da Kwankwaso, manyan ’yan siyasa da suka taɓa aiki tare a Kano amma daga baya suka rabu.

Abdulaziz, ya daɗe yana nesanta kansa daga tafiyar siyasar mahaifinsa, inda yake ci gaba da goyon bayan Kwankwasiyya.

Haka kuma, a baya ya taɓa samun saɓani da mahaifiyarsa, Farfesa Hafsat Umar Ganduje, har ya kai ƙararta ga EFCC kan wata matsala.

Zai yi takarar kujerar da ɗan uwansa ya tsaya a 2023 a ƙarƙashin APC amma ya sha kaye a hannun ɗan takarar NNPP, duk da kasancewar mahaifinsu gwamna a wancan lokaci.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000