Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su tare da kashe ‘ƴan ta’adda’biyar a wasu hare-haren da suka kai a jihohin Zamfara da Katsina.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar 29 ga Mayun 2026.
A cewar sanarwar, a Jihar Zamfara dakarun sun ceto mutanen ne a yankin Bagega zuwa Kawaye da ke ƙaramar hukumar Anka bayan wani samame ta sama da rundunar ta kai kan maɓoyar ‘yan ta’adda da ke yammacin dajin Bagega.
Mutanen da aka ceto sun fito ne daga ƙananan hukumomin Maga, Gummi, Zuru, Wasugu, Bukuyyum da Anka da ke jihohin Zamfara da Sokoto, bayan sun shafe makonni da dama a hannun masu garkuwa da mutane.
Rundunar ta ce an ba su kulawar lafiya kafin a mayar da su ga iyalansu.
Haka kuma, a wani samame ta daban a yankunan Maradun da Gidan Dan Jaja na Zamfara, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda inda suka kashe biyu daga cikinsu tare da lalata sansanoninsu.
Rundunar ta kuma ƙwato wasu bindigogi da aka ƙera a gida da kuma babura hudu da ake zargin masu laifin na amfani da su wajen gudanar da hare-hare.
A Jihar Katsina kuwa, dakarun sun tare wasu ‘yan ta’adda a yankunan Ruwan Godiya da titin Sayaya da ke ƙaramar hukumar Matazu yayin da suke kan hanyarsu ta kai hari.
Bayan musayar wuta mai zafi, sojojin sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da kwato babura da wasu harsasai.
