Kwamitin gwamnatin Jihar Kano dake yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ya gudanar da taronsa na farko, inda mambobinsa suka sake jaddada aniyarsu ta haɗa kai domin yaƙar shaye-shaye, safarar miyagun ƙwayoyi, fadan daba da sauran laifukan da ke da alaƙa da su a faɗin jihar.
Shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, ne ya jagoranci taron, wanda ya haɗa wakilan manyan ma’aikatun gwamnati, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da aka ɗora wa alhakin aiwatar da manufofin kwamitin.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tajo Usman; Kwamandan Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na Jihar Kano, Dr. Mustapha; Sakataren Zartarwa na Hukumar Kare Haƙƙin Mai saye da Mai sayarwa ta Kano; Shugaban sashin Ayyuka na Hukumar Tsaro ta DSS reshen Kano; Jami’in da ke jagorantar rundunar Anti-Daba ta jihar, tare da sauran mambobin kwamitin.
Da yake jawabi a wajen taron, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin samar da haɗin kai tsakanin hukumomi wajen magance matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da laifukan da ke da alaƙa da hakan a Jihar Kano.
Ya ce nasarar kwamitin za ta ta’allaka ne kan haɗin kai tsakanin hukumomin da ke cikinsa, da kuma jajircewar kowane ɓangare wajen sauke nauyin da aka ɗora masa cikin ƙwarewa, gaskiya da kishin ƙasa.
Barrista Muhuyi ya buƙaci mambobin kwamitin su mayar da hankali kan aikin da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ɗora musu, yana mai cewa yaƙi da shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi na buƙatar musayar bayanan sirri, yin hukunci kamar yadda doka ta ta nada, wayar da kan jama’a, shirye-shiryen gyaran masu ta’ammali da ƙwayoyi, da kuma ci gaba da haɗin gwiwa da al’ummomin jihar.
Ya ƙara da cewa kwamitin zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin matasa da shugabannin al’umma domin samar da dabaru masu ɗorewa da za su kare makomar matasan Kano tare da inganta zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

