• Home  
  • Kashi 70 na manyan laifuka a Kano na da alaƙa da shaye-shaye — Muhuyi
- Labarai

Kashi 70 na manyan laifuka a Kano na da alaƙa da shaye-shaye — Muhuyi

Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Yaƙi da Shaye-Shayen Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da ake aikatawa a jihar na da alaƙa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Rimin Gado ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da manema labarai a Kano, inda ya […]

Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Yaƙi da Shaye-Shayen Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da ake aikatawa a jihar na da alaƙa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Rimin Gado ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da manema labarai a Kano, inda ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su goyi bayan yaƙin da gwamnati ke yi da shaye-shaye, fataucin miyagun ƙwayoyi da ayyukan daba ta hanyar wayar da kan al’umma.

Ya ce an kafa kwamitin ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a matsayin matsalar gaggawa ta lafiyar al’umma a jihar, tare da ba shi alhakin yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, kula da masu fama da jaraba da kuma gurfanar da masu laifi.

A cewarsa, dabarun kwamitin ba su taƙaita ga kama masu laifi kaɗai ba, har ma sun haɗa da rigakafi, gyaran hali da haɗa kan al’umma.

Ya ce alƙaluman Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano sun nuna cewa daga cikin mutum 3,080 da aka kama da manyan laifuka a shekarar da ta gabata, kusan kashi 70.2 cikin 100 na laifukan na da alaƙa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Ya ce, “Da a ce an shawo kan matsalar shaye-shaye tun da wuri, da yawancin waɗannan laifuka ba su faru ba. Wannan ne ya sa gwamnati ta ƙuduri aniyar magance matsalar ta hanyar wannan kwamitin haɗin gwiwa.”

Rimin Gado ya ce kwamitin zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da al’umma, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin magance tushen shaye-shaye da laifukan da ke da alaƙa da su.

Ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnati za ta hukunta duk wanda aka samu yana da hannu a ayyukan daba ko wasu laifukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro.

A cewarsa, kwamitin zai ƙara ƙaimi wajen tarwatsa hanyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da tabbatar da cewa masu fama da jaraba sun samu kulawa da gyaran hali.

Haka kuma, ya yi kira ga iyaye su ƙara sanya ido kan tarbiyyar ’ya’yansu domin kare su daga faɗawa shaye-shaye da miyagun laifuka.

Ya ce, “’Ya’yanmu su ne makomar wannan al’umma. Wajibi ne mu ba su tarbiyya tare da kare su daga shaye-shaye da aikata laifuka.”

Rimin Gado ya kuma roƙi manema labarai su ci gaba da haɗa hannu da kwamitin wajen wayar da kan jama’a game da illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen sauya tunanin al’umma da ƙarfafa goyon bayan yaƙin da ake yi da wannan annoba.

Ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da haɗa gwiwa da kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa ƙoƙarin rage shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da inganta tsaron al’umma a Jihar Kano.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000