Afirka ta Kudu na fuskantar ƙarancin ma’aikata bayan da fiye da baƙi 160,000 ne suka bar ƙasar sakamakon hare-haren da ake kai musu da kuma zanga-zangar ƙyamar da tsaurara matakan shige da fice.
Lamarin ya fara shafar fannoni kamar noma, gine-gine, aikin gida da masana’antu, inda masu ɗaukar aiki ke kokawa kan rashin ma’aikatan da za su maye gurbin waɗanda suka tafi.
Manoma da masu masana’antu sun ce ficewar ƙwararrun ma’aikatan ƙasashen waje na barazana ga yawan amfanin da suke samarwa, yayin da ƙungiyoyin ƙwadago ke zargin wasu kamfanoni da fifita baƙi saboda albashinsu ya fi rahusa.
A halin yanzu, gwamnatin ƙasar na neman hanyar da za ta daidaita buƙatar samar da ayyukan yi ga ‘yan ƙasa da kuma buƙatar wasu sassa da ke dogaro da ma’aikatan ƙasashen waje.
Yawancin waɗanda suka fice daga ƙasar sun ce sun yi hakan ne saboda tsoron hare-haren ƙin jinin baƙi da kuma farmakin jami’an tsaro kan waɗanda ba su da takardun zama.
