Aƙalla mutane biyar ne suka mutu, yayin da aka ceto wasu tara bayan rushewar wasu gine-gine biyu a sassa daban-daban na Jihar Kano a ranar Asabar, sakamakon ruwan sama mai ƙarfi.
Ginin farko ya rushe ne a yankin Gaida Sabon Titi, a kan hanyar gidan man Salbas da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, inda wani bene mai hawa biyu da ake ginawa ya rushe, yayin da ake ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Wani ganau, Idris Mustapha Nasir, ya shaida wa wakilanmu cewa ana kyautata zaton wasu mutane sun maƙale a ƙarƙashin tarkacen ginin.
Ya ce jami’an kashe gobara tare da taimakon mazauna yankin, sun yi aikin ceto nan take.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa daga baya likitoci a Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed da ke Kano sun tabbatar da mutuwar mutane huɗu.
Ya bayyana sunayen mamatan da suka haɗa da Sunusi Surajo, mai shekara 18; Bashir Ibrahim, mai shekara 20; Ibrahim Ibrahim, mai shekara 25; da Abubakar Mohammed, mai shekara 30. Dukkansu ma’aikata ne da ke aikin gini.
Saminu ya ce wani ginin kuma ya rushe a wata makarantar Islamiyya a yankin Kurna, wadda aka fi sani da Khadijah Idris Bala School, a lokacin da ake tsaka da da karatu.
A cewarsa, mutane tara ne abin ya shafa, inda aka ceto mutum takwas, yayin da likitoci suka tabbatar da mutuwar wata ɗaliba mai shekara 13, mai suna Khadijah Mohammed.
Kakakin hukumar kashe gobarar ya buƙaci mazauna jihar, musamman injiniyoyin gine-gine, ’yan kwangila da ma’aikata, da su ƙara yin taka-tsantsan a lokacin damina domin kauce wa sake asarar rayuka.
Ya kuma shawarci jama’a da su guji zama a ciki ko kusa da gine-ginen da ake zargin ba su da ƙarfi ko ingantaccen tsari a lokacin da ake ruwan sama mai ƙarfi.
