• Home  
  • Gwamnatin Jigawa ta fara gina sabuwar fadar Sarkin Dutse kan N2.6bn
- Labarai

Gwamnatin Jigawa ta fara gina sabuwar fadar Sarkin Dutse kan N2.6bn

Gwamnatin Jihar Jigawa ta mika filin da za a gina sabuwar fadar Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammad Nuhu Sanusi, da aka ware sama da Naira biliyan 2.6. Da yake jagorantar mika filin filin da ke unguwar Bokoto, daura da Babban Masallacin Dutse, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya ce gina sabuwar fadar na […]

Gwamnatin Jihar Jigawa ta mika filin da za a gina sabuwar fadar Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammad Nuhu Sanusi, da aka ware sama da Naira biliyan 2.6.

Da yake jagorantar mika filin filin da ke unguwar Bokoto, daura da Babban Masallacin Dutse, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya ce gina sabuwar fadar na daga cikin matakan da gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi ke dauka domin karfafa alaka da masarautun gargajiya a fadin jihar.

Ya bayyana sarakunan gargajiya a matsayin muhimman abokan gwamnati wajen samar da zaman lafiya, sulhu da bunkasa al’umma, yana mai cewa rawar da suke takawa na da matukar muhimmanci wajen ci-gaba da zaman lafiyar jihar.

Ya ce ko da yake gwamnatin tsohon Gwamna Ali Sa’ad Birnin Kudu ce ta ware filin da za a gudanar da aikin, amma gwamnatin yanzu ce ta bayar da kwangilar fara aikin.

A cewarsa, wannan aiki ya nuna irin girman darajar da Gwamnatin Namadi ke bai wa masarautun gargajiya, da kuma kudirinta na samar musu da yanayin da zai ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya bukaci kamfanin da ya samu kwangilar aikin, NEWPRO QUANTS CONSULTANCY NIGERIA LIMITED, da ya bi dukkan ka’idoji da bayanan aikin da aka amince da su, tare da tabbatar da kammala aikin cikin wa’adin da aka kayyade.

Da yake mayar da jawabi, wakilin kamfanin, Alhaji Buhari Abdulkadir Kawu, ya tabbatar wa gwamnati cewa za su gudanar da aikin bisa kwarewa da ka’idojin aikin gini.

Ya ce kamfanin zai tabbatar da cewa sabuwar fadar ta kasance wuri mai bayyana muhimmancin al’adu da tarihin Masarautar Dutse, tare da hada su da tsarin gine-ginen zamani.

Shi ma mai ba da shawara kan aikin, Akitet Aliyu Kaila na Integral Consultancy Company, ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su bi ka’idojin kwangilar yadda ya kamata domin tabbatar da kammala aikin cikin lokaci.

Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Babban Sakataren Gudanarwa da Harkokin Kudi a Ofishin SSG, Alhaji Abdullahi Sa’idu, ya bayyana mika wurin aikin a matsayin wani muhimmin mataki na fara aikin gina sabuwar fadar.

Ya ce aikin wani karin mataki ne da gwamnatin Namadi ta dauka wajen samar da kyakkyawan yanayi da zai taimaka wa masarautun gargajiya wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Darakta-Janar na Hukumar Sa Ido Kan Bin Ka’idar Aiki, Farfesa Kasim Muhammad, wanda Dakta Usman Musa ya wakilta, ya bukaci kamfanin da ya kammala aikin bisa jadawalin da aka tsara tare da bin dukkan bayanan kwangilar.

Ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da inganci, gaskiya da amfani da kudaden gwamnati yadda ya kamata, yana mai gargadin cewa ba za a amince da aikin da bai kai matsayin da ake bukata ba.

A nasa bangaren, Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammad Nuhu Sanusi, wanda Magatakardan Dutse, Alhaji Ahmadu Malami, ya wakilta, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa wannan muhimmin shiri.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai