• Home  
  • Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro
- Labarai

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro Ƙungiyar Kanawa Mazauna Birnin Tarayya Abuja ta gudanar da wani babban taro a ranar Lahadi, wanda ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga ƙananan hukumomin birnin. Shugaban Kanawa Mazauna Abuja Initiative Group, Alhaji Ali Baba, ya ce wannan ne karon farko da ƙungiyar ta gudanar da irin wannan […]

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro

Ƙungiyar Kanawa Mazauna Birnin Tarayya Abuja ta gudanar da wani babban taro a ranar Lahadi, wanda ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga ƙananan hukumomin birnin.

Shugaban Kanawa Mazauna Abuja Initiative Group, Alhaji Ali Baba, ya ce wannan ne karon farko da ƙungiyar ta gudanar da irin wannan babban taro tare da haɗin kan mambobinta.

Ya ce manufar ƙungiyar ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta, taimaka wa al’umma da kuma inganta zumunci da fahimtar juna.

kungiyar dai tana burin taimakawa al’umma da samarwa da daliban suka kammala karatu guraben aiki a ma’aikatun gwamnati da kuma kamafanoni masu zaman kansu harma da tallafa musu da jari don dogaro da kansu.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana gamsuwarsu da yadda taron ya gudana, tare da yin alkawarin ci gaba da bai wa ƙungiyar goyon baya domin ganin ta cimma manufofinta.

Taron ya gudana cikin yanayi na annashuwa, inda mahalarta suka samu damar tattaunawa da juna tare da ƙarfafa zumuncin da ke tsakaninsu.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000