• Home  
  • Rimingado ya kaddamar da kwamitoci 9 da kan yaki da miyagun kwayoyi a Kano.
- Labarai

Rimingado ya kaddamar da kwamitoci 9 da kan yaki da miyagun kwayoyi a Kano.

Shugaban kwamitin haɗin gwiwar hukumomi ta yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a Kano, Muhuyi Rimingado, ya ƙaddamar da kwamitoci tara domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi a jihar. Rimingado ya buƙaci mambobin kwamitocin da su kasance masu jajircewa, tare da aiki kafada da kafada wajen ganin an cimma manufofin rundunar. […]

Shugaban kwamitin haɗin gwiwar hukumomi ta yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a Kano, Muhuyi Rimingado, ya ƙaddamar da kwamitoci tara domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Rimingado ya buƙaci mambobin kwamitocin da su kasance masu jajircewa, tare da aiki kafada da kafada wajen ganin an cimma manufofin rundunar.

Ya ce nasarar yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi na buƙatar haɗin gwiwa, kyakkyawan tsari da ɗaukar nauyin kowa.

Ya bayyana cewa an kafa kwamitocin ne domin samar da ingantaccen tsarin tunkarar matsalar miyagun ƙwayoyi da kuma haɗa kan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.

An ƙaddamar da kwamitocin ne a ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000