• Home  
  • Tinubu da gwamnoni sun kafa kwamitin lalubo hanyoyin rage tsadar sufuri
- Babban Labari

Tinubu da gwamnoni sun kafa kwamitin lalubo hanyoyin rage tsadar sufuri

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya amince da kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin aiwatar da matakan rage tsadar sufuri a faɗin ƙasar. Tinubu ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da ƙungiyar gwamnonin Najeriya, inda ya ce gwamnonin sun ɗauki matakin rage kuɗin sufuri a jihohinsu, musamman ta hanyar […]

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya amince da kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin aiwatar da matakan rage tsadar sufuri a faɗin ƙasar.

Tinubu ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da ƙungiyar gwamnonin Najeriya, inda ya ce gwamnonin sun ɗauki matakin rage kuɗin sufuri a jihohinsu, musamman ta hanyar amfani da motocin CNG da na lantarki.

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce gwamnatin tarayya ma na zuba jari mai yawa wajen sauya tsarin makamashin sufuri, ciki har da shirin shugaban ƙasa na CNG, inda aka sauya motocin sama da 120,000 daga amfani da man fetur zuwa CNG.

Tinubu ya ce akwai kuma wasu kayan sauya motocin sama da 100,000 da ake shirin kammalawa, yayin da ake ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin sauya motocin da wuraren da ake samun CNG a faɗin ƙasar.

Shugaban ya ce ya kuma bayar da umarnin ƙara samar da wasu tashoshin CNG 500 a faɗin ƙasar, baya ga 500 da aka riga aka ba da umarnin samarwa a farkon shekarar.

“Muna fatan daga ranar 1 ga Oktoba, ’yan Najeriya su fara cin moriyar wannan tanadi ta hanyar samun sauƙin kuɗin sufuri,” in ji Tinubu.

Tinubu ya ce gwamnati ta tarayya da jihohi sun amince da fara aiwatar da matakan nan take, domin tabbatar da cewa an samu raguwar kuɗin man fetur domin samun sauƙin kuɗin sufuri.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000