Kotun shari’ar addinin musulunci dake zamanta a Jogana, ta umarci hukumar gidan a jiya da gyaran hali ta kasa reshen jihar Kano, ta bayar dukkan wata kulawa da ta kamata ga Yusuf Mahmud Rano, wanda ya datse dan yatsansa da wuka bayan an kwadaita masa samun naira miliyan 80.
Kotun ta sanya wannan rana ta Litinin domin yin hukunci, amma ta ce ba zata samu damar yanke hukuncin ba, kasancewar lauyoyin gwamnati za su shiga cikin wannan magana.
Alƙalin kotun mai shari’a, Kamalu Haruna, ya dage shari’ar zuwa ranar Alhamis 17 ga watan Satumba 2026, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar na 1,2,3 da na 4 a gidan yari zuwa ranar.
Haka zalika kotun ta yi umarnin hukumar gidan gyaran hali da tarbiya ta bayar da dukkan wata kulawa ga Yusuf Mahmud Rano.
Tunda farko rundunar yan sandan jihar Kano, ce ta gurfanar da, Abdurraham Abbas Kwasamgwami Gezawa, Sha’aibu Yawale Daganawa Bunkure, Abubakar Iliyasu Zangon Dakata, Ishaq Isah Rano da kuma Yusuf Mahmud Rano, bisa zargin hada kai da yunkurin aikata tsafi.
A zaman kotun da ya gabata wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu.
