Kotun musulunci dake Jogana ta bayar da umarnin tsare mutanen da Ake tuhuma da yunkurin aikata tsafi.
Kotun shari’ar addinin musulunci dake zamanta a unguwar Jogana Kano, karkashin jagorancin mai shari’a, Kamalu Haruna, ta bayar da umarnin tsare mutanen da ake zargi da hada kai da yunkurin aikata tsafi. Wadanda ake tuhumar sun hada da, Yusuf Mahmud mazaunin Rano, Abdurraham Abbas mazaunin Kwasamgwami Gezawa da Sha’aibu Yawale Daganawa Bunkure da Abubakar Iliyasu […]


