Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta musanta zargin cewa an karkatar da kujerun Hajjin 2027, inda ta ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa an karya dokokin Saudiyya ko ƙa’idojin hukumar wajen rabon kujerun.
Wannan na zuwa ne bayan wata takardar ƙorafi da wasu masu gudanar da aikin Hajji masu zaman kansu suka yi, inda suka buƙaci a binciki zargin karkatar da kujerun Hajji 5,000.
A wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai NAHCON Shafii Sani Mohammed, ya fitar ta ce Najeriya ta samu kujerun Hajji 50,000 na shekarar 2027, inda aka ware 35,000 ga jihohi da Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da aka ware 15,000 ga kamfanonin Hajji masu zaman kansu.
Hukumar ta ce an raba kujerun kamfanoni masu zaman kansu ne ga masu gudanar da aikin Hajji da ke ƙarƙashin manyan kamfanoni bakwai da aka amince da su, bisa ƙa’idojin Najeriya da na Saudiyya.
NAHCON ta kuma ce wasu daga cikin masu gudanar da aikin Hajjin na fuskantar ƙalubale wajen cika ƙa’dojin da Saudiyya ta gindaya na Nusuk-Masar, wanda wa’adin shigar da bayanan mahajjata zai ƙare a ranar 26 ga Satumba 2026.
Ta ce ba ta da ikon tsawaita wannan wa’adin da gwamnatin Saudiyya ta gindaya.
Hukumar ta buƙaci mahajjatan da suka yi rajista ta hannun kamfanoni masu zaman kansu su tabbatar da cewa an kammala shigar da bayanan rajistarsu da na yatsunsu cikin tsarin Nusuk kafin wa’adin.
NAHCON ta ce za ta ɗauki matakin ladabtarwa, ciki har da dakatar da lasisi ko soke shi, kan kamfanonin da suka kasa sauke nauyin da ke kansu cikin wa’adin da aka kayyade.
Hukumar ta ce iƙirarin karkatar da kujerun za su ci gaba da kasancewa zarge-zarge ne matuƙar ba a gabatar da hujjar da ke nuna an karya wata doka ko ƙa’ida ba.
