Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Habibu Bello, mai shekaru 35, da ake zargi da kasancewa cikin kungiyar masu garkuwa da mutane, fashi da makami da satar shanu da ke aiki tsakanin jahohin Kano, Kaduna da Katsina.
An kama shi ne a ranar 14 ga Satumba, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri, yayin da bincike ya kai ga kama wani mai suna ,Mudam mazaunin Kwanar Dangora, wanda ake zargi da kasancewa cikin kungiyar.
Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a wasu hare-haren garkuwa da mutane, ciki har da sace Hajiya Binta daga Kwanar Dangora, inda aka biya Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.
A wani samame kuma, ’yan sanda sun gano drone mai daukar hoto mai lamba GT 50 a Hawan Tarau, karamar hukumar Bebeji, yayin da ake ci gaba da kokarin gano mai drone din.
Kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an tare da cewa za a ci gaba da aikin simame musamman a kan iyakokin Kano da jihohin makwabta.