• Home  
  • Ba na jin haushin abokaina da suka yi shiru kan tsare ni — El-Rufai 
- Labarai

Ba na jin haushin abokaina da suka yi shiru kan tsare ni — El-Rufai 

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ba ya jin haushin abokansa, abokan aiki da mutanen da ya taɓa taimakawa da suka yi shiru kan halin da yake ciki a yanzu. A cikin wata sanarwa mai taken “My Relationships and the Aftermath”, El-Rufai ya ce wasu mutane sun nuna damuwa game da yadda mutanen […]

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ba ya jin haushin abokansa, abokan aiki da mutanen da ya taɓa taimakawa da suka yi shiru kan halin da yake ciki a yanzu.

A cikin wata sanarwa mai taken “My Relationships and the Aftermath”, El-Rufai ya ce wasu mutane sun nuna damuwa game da yadda mutanen da ya taɓa taimakawa ko hulɗa da su a baya suka yi shiru a lokacin da yake fuskantar ƙalubale.

Ya ce goyon bayan da yake bai wa mutane da wasu manufofi a baya ya samo asali ne daga addininsa na Musulunci, tarbiyyar Arewa, ɗabi’unsa.

Ya kuma ce ya yi abin da yake ganin shi ne daidai, ba wai domin a yabe shi ko a masa sakayya ba.

“A tsawon shekarun da na kasance tare da mutane kuma na goyi bayan abubuwan da na yi imani da su, wani lokacin su kan kasance masu wuyar sha’ani ko su haifar min da matsala.”

Tsohon gwamnan ya ce mutanen da ya taɓa taimakawa suna da ’yancin zaɓar su fito su mara masa baya ko kuma su yi shiru.

“Dalilannsu nasu ne, kuma ba na son yin hukunci a kansu saboda kawai martaninsu ya bambanta da abin da wasu ko ni kaina na yi tsammani.”

El-Rufai ya ce mawuyacin halin da ya shiga a cikin ’yan watannin da suka gabata ya taimaka masa wajen fahimtar wasu daga cikin alaƙarsa da mutane.

“Matsala tana da hanyar bayyana ainihin yanayin alaƙar da ke tsakaninka da mutane.”

Ya ce yana iya sake duba yanayin alaƙarsa da wasu, amma ba don yana jin haushi ko neman ɗaukar fansa ba.

El-Rufai ya kuma jaddada cewa bai yi nadamar taimaka wa mutane a lokacin da ya yi imanin cewa abin da ya dace shi ne ya taimaka ba.

“Ba na jin haushin duk wanda ya zaɓi ka da ya yi min irin abin da na taɓa yi masa.”

Tsohon gwamnan, wanda ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da farautarsa saboda siyasa, ya ce ba ya neman ɗaukar fansa kan duk wani abin da yake ganin an yi masa na rashin adalci.

“Babban hukunci yana hannun Allah Maɗaukakin Sarki, kuma na bar wannan hukunci a hannunsa, a duniya da kuma lahira.”

El-Rufai ya ce abin da ya fi damunsa shi ne ya ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da kuma kusantar Ubangiji.

“Abin da ya fi damuna shi ne na kasance cikin kwanciyar hankali a lamirina, kuma sama da komai, da Allah Maɗaukakin Sarki.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai