• Home  
  • Kotu ta tsare matasa 11 da ake zargi da kashe dan sanda a Kano
- Labarai

Kotu ta tsare matasa 11 da ake zargi da kashe dan sanda a Kano

Kotun majistret mai lamba 2 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman, ta aike da wasu matasa 11 gidan gyaran hali. Ana dai zargin matasan ne da laifin haɗa baki da tayar da hankalin al’umma da kuma ƙeta ta hanyar kunna wuta a kan kayan mutane, da kuma kashe jam’i’in ƴan sanda. Ƙunshin zargin ya […]

Kotun majistret mai lamba 2 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman, ta aike da wasu matasa 11 gidan gyaran hali.
Ana dai zargin matasan ne da laifin haɗa baki da tayar da hankalin al’umma da kuma ƙeta ta hanyar kunna wuta a kan kayan mutane, da kuma kashe jam’i’in ƴan sanda.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar an samu rashin fahimtar juna akan batun iyakar gona a ƙaramar hukumar Wudil da ke Kano, lokacin da yansanda suka je wajen domin tabbatar da doka da oda, inda aka yi zargin cewar wasu matasa goma sha ɗaya sun haɗa baki sun kashe wani ɗansanda.
Manema labarai sun ruwaito cewa an kuma zargi matasan da laifin cinna wuta a kan kayan al’umma.
A ƙarshe, Kotun ta bayyana cewar bata da hurumin yin shari’ar kisan kai sai an jira shawararin lauyoyin gwamnati, inda aka sanya ranar 15 ga watan Oktoba domin ƙara gabatar da matasan

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai