Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai ƙaddamar da fara sabon titin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Kano a wata mai zuwa.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya ce shugaban Tinubu zai ƙaddamar da sabin titin a ranar 3 ga watan Disamba mai zuwa.
Aikin layin dogo mai tsawon kilomita 203 daga Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano, wanda yana ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin, ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammaluwa, yayin da aikin layin dogo mai tsawon kilomita 400 daga Kano zuwa Katsina da Maradi ya kai kashi 70 cikin 100 na kammaluwa.
Layin dogon Kaduna zuwa Kano, wanda ƙari ne ga layin dogon da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, zai samar da ci gaba da haɗin layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna da Zaria da Kano da tare da ƙarfafa hanyoyin sufuri tsakanin manyan cibiyoyin kasuwanci a Arewacin Najeriya.
Kwanan nan wata tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Injiniya Funso Adebiyi, ta duba waɗannan ayyukan layin dogo guda biyu bisa umarnin Shugaba Tinubu, inda ya bayyana gamsuwarsa da ingancin aikin ginin, musamman dangane da shimfiɗar layin dogo, ababen zubar da ruwa da kariyar ginin tudu da shimfiɗar duwatsu da kuma daidaita ƙasa.
Binciken ya haɗa da gwajin tafiyar jirgin ƙasa daga Jaji a Jihar Kaduna zuwa Kano, wanda ya bai wa jami’ai damar tantance kayayyakin ingancin layin dogon da aka kammala haɗe da abubuwan more rayuwa da aka tanada.
