Kamfanin Tianneng ya ƙaddamar da sabbin babura masu kafa biyu da masu kafa uku, waɗanda ke amfani da wutar lantarki, a wani biki da ya gudana a nan Kano.

Taron ƙaddamar ya samu halartar manyan ’yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci a jihar Kano, ciki har da Alhaji Sabiu Bako da Alhaji Tajjudin Aminu Dantata, tare da sauran manyan ’yan kasuwa.
A yayin taron, kamfanin ya bayyana wasu daga cikin sabbin fasahohin da ya zo da su, musamman motocin hawa masu amfani da lantarki, waɗanda ake sa ran za su ƙara saukaka hanyoyin sufuri ga masu amfani da ababen hawa a jihar.
Haka kuma, kamfanin Tianneng ya kulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da wasu kamfanoni a nan Kano, domin bunƙasa kasuwancinsa da faɗaɗa amfani da kayayyakin da kamfanin ke samarwa a kasuwannin Kano da sauran sassan ƙasar nan.
Taron ya kuma kasance wata dama ta haɗa kamfanin da ’yan kasuwa da masu zuba jari, domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa da kuma bunƙasa harkokin sufuri masu amfani da makamashin lantarki.
