• Home  
  • ‘Masar za ta taimaki Saudiyya wajen kariya idan ta buƙaci haka’
- Kasashen Ketare

‘Masar za ta taimaki Saudiyya wajen kariya idan ta buƙaci haka’

Shugaban ƙasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya ce ƙasarsa za ta ɗauki duk wani mataki da ya dace domin kare Saudiyya idan mahukuntan Riyadh suka nemi hakan. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren da ƙungiyar Houthi ke kai wa Saudiyya suka ƙaru. “Ba zai yiwu mu amince a cutar da Saudiyya […]

Shugaban ƙasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya ce ƙasarsa za ta ɗauki duk wani mataki da ya dace domin kare Saudiyya idan mahukuntan Riyadh suka nemi hakan.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren da ƙungiyar Houthi ke kai wa Saudiyya suka ƙaru.

“Ba zai yiwu mu amince a cutar da Saudiyya ko kuma a kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyarta ba,” in ji Mista Sisi yayin bikin yaye ɗalibai a Kwalejin Sojin Masar.

Ya jaddada cewa Masar ba ta neman kai wa kowace ƙasa hari, amma a shirye take ta ɗauki matakin kare Saudiyya idan bukatar hakan ta taso.

A kwanakin baya, mayaƙan Houthi na Yemen, waɗanda ke samun goyon bayan Iran, sun kai hare-hare kan Filin Jirgin Sama na Riyadh da kuma kamfanin mai na ƙasar Saudi Aramco.

Hare-haren sun zo ne bayan da aka sake komawa rikici tsakanin mayakan Houthi da dakarun gwamnatin Yemen masu samun goyon bayan Saudiyya.

Shugaba Sisi ya ce Masar za ta yi aiki ne bisa jagoranci da umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz da kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.

Jami’an Saudiyyar biyu sun gana da Shugaba Sisi a ranar 15 ga Satumba, bayan sake ɓarkewar faɗa a Yemen, inda suka tattauna batutuwan tsaro da zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya (Red Sea) da sauran muhimman batutuwa.

A wani ɓangare na jawabinsa, Sisi ya ce: “Na san cewa irin wannan mataki yana buƙatar amincewar Majalisar Dokokin Masar. Saboda haka, ina neman a kira zaman gaggawa domin ba mu izinin da ake buƙata idan Saudiyya ta nemi mu ɗauki mataki.”

Jim kaɗan bayan wannan jawabi, Majalisar Dokokin Masar ta sanar da cewa za ta gudanar da zaman musamman gobe domin duba buƙatar da shugaban ƙasar ya gabatar, kodayake ba a bayyana ajandar zaman ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai