• Home  
  • Cutar Ebola da aka gano a Najeriya na kama da wadda ta ɓarke a Kenya
- Labarai - Lafiya

Cutar Ebola da aka gano a Najeriya na kama da wadda ta ɓarke a Kenya

Ministan Lafiya na Najeriya, Muhammad Ali Pate, ya ce binciken ƙwayoyin halittar wadda aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Najeriya ya nuna cewa ƙwayar cutar tana da kamanceceniya sosai da nau’in cutar da aka gano a mutum na farko da ya kamu da ita a Kenya. Wannan shi ne karo na farko da […]

Ministan Lafiya na Najeriya, Muhammad Ali Pate, ya ce binciken ƙwayoyin halittar wadda aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Najeriya ya nuna cewa ƙwayar cutar tana da kamanceceniya sosai da nau’in cutar da aka gano a mutum na farko da ya kamu da ita a Kenya.

Wannan shi ne karo na farko da aka samu wata hujjar kimiyya da ke nuna alaƙa tsakanin ɓarkewar cutar a ƙasashen biyu.

Sai dai hukumomin Najeriya sun ce babu wata shaida da ke nuna cewa mutumin farko da ya kamu da Ebola a Kenya ya taɓa zuwa Najeriya ko kuma yana da wata alaƙa kai tsaye da wanda aka gano da cutar a Najeriya.

Minista Pate ya ce hukumomi na ci gaba da gano da bibiyar duk waɗanda suka yi hulɗa da wanda ya kamu da cutar, inda ake killace su tare da yi musu gwaji. Ya ce wasu daga cikin sakamakon gwaje-gwajen sun fito babu cutar, yayin da ake jiran sakamakon wasu.

Najeriya dai ta tabbatar da mutum guda kacal da ya kamu da Ebola, wanda rahotanni suka ce ya yi tafiya zuwa ƙasar Uganda kafin a gano yana ɗauke da cutar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai