A wani sakamako da ya bai wa mutane da dama mamaki, wata ƙungiyar ɗalibai masu zanga-zangar neman sauyi ce ta lashe babban zaɓen ƙasar Serbia, inda ta doke tsohon shugaban ƙasar Aleksandar Vucic, wanda ya shafe shekaru 14 yana mulki.
Bayan da Mista Vucic ya amince da shan kaye, dubban magoya bayan ‘yan dawa sun fito kan titunan birnin Belgrade suna ta shagulgula.
Yawan waɗanda suka fito kaɗa ƙuri’a ya kai kusan kashi 70 cikin 100, wanda ya zamo mafi yawa a cikin gwamman shekaru.
Wakilin BBC da ke Belgrade ya ce har yanzu ba a san cikakkun bayanai a kan yadda ƙungiyar ɗaliban ta tsara ayyukanta ba, haka kuma ba a san wanene zai zama sabon firaministan ƙasar ko manufofin da sabuwar gwamnati za ta bi ba.

