Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kebbi ta yi nasarar kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su ta kuma kama wasu mutum uku da ake zargi bayan wani samame da suka kai a garin Dakingari a Karamar Hukumar Suru ta Jihar Kebbi.
‘Yan sanda sun kai samamen ne bayan sun samu bayani ingantacce na cewa, ‘yan bindiga sun shiga kauyen Dolen Kwandage har sun yi, garkuwa da mutum uku wato Sama’ila Abubakar dan shekara 35 da Dayyaba Muhammadu mai shekara 32 da Balki Hakimi ‘yar shekara 31.
Sun kuma shiga kauyen Yarma suka tafi da wani mai suna Mo’e Muddaha da Hadiza Bello wadanda dukan su tsofaffi ne.
A bayanin da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar. SP Bashir Usman ya fitar ranar Lahadi ya ce, da samun bayanin aukuwar lamarin, jami’ansu ba su yi sanyin jiki ba suka tunkari maharan abin da a sanya suka bar mutanen da suka sato mata hudu da namiji daya.
“Duka mutum biyar da aka tseratar an kai su Babban Asibitin Dakingari inda aka ba su kulawa sanan aka mayar da su cikin danginsu.”
Ya ce, samamen ya ba da nasarar kama wasu da ake zargi su uku, Umaru Janyo mai shekara 49 da Bube Kwaire matashi dan shekara 28, wadanda su ‘yan kauyen Bendu ne, sai Muhammadu Gyade matashi dan shekara 22 da ya fito daga Tindifai.
“Wasu daga cikin wadanda muke zargi sun tsere da raunin halbi a jikinsu, sai dai mun kwato babur Haju da kudi Naira dubu 308 da kaca da jarka.”
Jami’in ya ce, jami’ansu na kan sintiri a yankin domin ganin sun kama wadanda suka gudu domin tabbatar da an hukunta su.
Ya ce, kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kebbi CP Umar M. Hadeja ya jinjina wa jami’an da ‘yan banga kan hadin kai da kwarin gwiwarsu a wurin tabbatar da sun tarwatsa bata-garin.
Ya yi kira ga mutanen gari su ci gaba da bayar da bayani kan lokaci ga jami’an tsaro domin karfafa aikin da suke yi na samar da zaman lafiya.
