• Home  
  • Abuja: An Fara Rufe Hanyoyi Domin Tabbatar da Tsaro a Ranar Rantsar da Sabon Shugaban Ƙasa
- Labarai

Abuja: An Fara Rufe Hanyoyi Domin Tabbatar da Tsaro a Ranar Rantsar da Sabon Shugaban Ƙasa

Hukumomi a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, sun ba da izinin rufe wasu hanyoyi da suka dangana da gine-ginen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar saboda faretin rantsar da sabuwar gwamnati da za a yi.

Za a rufe hanyoyin ne daga ranar Juma’a 26 ga watan Mayu da misalin karfe 2 na rana har sai ranar 29 ga watan Mayu kamar yadda rahotanni suka nuna.

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da zababben Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Rahotanni sun ruwaito Sakatariyar walwala a ofishin ma’aikatan gwamnatin tarayyar Dr. Ngozi Onwudiwe a matsayin wacce ta sanar da shirin daukan matakin rufe wasu hanyoyin a birnin.

A cewar Mrs. Onwudiwe, umurnin rufe hanyoyin na da nasaba da matakan tsaro da kwamitin karbar mika mulki da shugaban kasa ya kafa ya dauka, don a tabbatar bikin ya gudana ba tare da wata tangarda ba.

Wasu kafafen yada labaran Najeriya sun ruwaito cewa ba za a bude hanyoyin ba sai ranar 30 ga watan Mayu, kwana guda bayan an kammala bikin rantsar da sabuwar gwamatin Tinubu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai