• Home  
  • Angola: ‘Yan sanda sun tarwatsa mutanen dake zanga-zanga kan karin farashin man fetur
- Kasashen Ketare - Labarai

Angola: ‘Yan sanda sun tarwatsa mutanen dake zanga-zanga kan karin farashin man fetur

‘Yan sanda a Angola sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun mutanen da suka fito suna zanga-zanga kan karin farashin man fetur a ƙasar.

Angola: 'Yan sanda kasar sun tarwatsa mutanen dake zanga-zanga kan karin farashin man fetur

‘Yan sanda a Angola sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun mutanen da suka fito suna zanga-zanga kan karin farashin man fetur a ƙasar.

Dubban mutane sun fantsama kan tittuna a birnin Luanda da sauran manyan birane.

Angola da ke ta biyu a arzikin man fetur a Afirka – ta zabtare kuɗin tallafin da take bayarwa a fetur a watan da ya gabata, lamarin da ya ninka farashin a gidajen mai.

‘Yan adawa da ƙungiyoyin fararan-hula sun ce an yi gaggawa wajen cire tallafin, tare da kira ga ‘yan sanda su daina amfani da ƙarfi kan masu bore.

A makon da ya gabata mutum biyar aka kashe lokacin da ‘yan sanda suka buɗe wuta kan direbobin tasi da babura da ke zanga-zanga.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai