Al’ummar Mali sun fita rumfunan zabe domin kada kuri’ar raba gardama a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar da sojojin suka yi wa gyaran fuska domin mayar da kasar a kan tafarkin mulkin dimukradiyya.
An bude rumfunan zaben da misalin karfe 8 agogon GMT, yayin da ake sa ran samun cikakken sakamako bayan sa’o’i 72.
Sabon kundin tsarin mulkin da al’ummar Mali sama da miliyan 8 ke kada kuri’ar amincewa ko kuma akasin haka shi ne mataki na farko da sojojin ke yi na tsawaita mulkinsu har zuwa shekarar 2024.
Kasar da ke yammacin Afirka ta kwashe shekarun uku tana karkashin ikon sojoji da suka kifar da halastaciyar gwamatin farar hula ta Ibrahim Boubakar Keita a shekarar 2020.
Batu na tsaro na daga cikin manyan kalubalen da kasar ke fama da shi tun bayan barkewar rikicin ‘yan ta’adda da na ‘yan aware a shekarar 2012.