• Home  
  • Tsananin zafin rana ya tilasta kwantar da alhazai fiye da 4,000 a asibitoci a saudiyya
- Labarai

Tsananin zafin rana ya tilasta kwantar da alhazai fiye da 4,000 a asibitoci a saudiyya

Alhazai fiye da dubu hudu aka kwantar a asibiti sakamakon tsananin zafin rana a yayin aikin hajjin bana, cewar mai wani Magana da yawun ma’aikatar lafiya ta kasar a jiya laraba.

Tsananin zafin rana ya tilasta kwantar da alhazai fiye da 4,000 asibitoci a saudiyya

Alhazai fiye da dubu hudu aka kwantar a asibiti sakamakon tsananin zafin rana a yayin aikin hajjin bana, cewar mai wani Magana da yawun ma’aikatar lafiya ta kasar a jiya laraba.

Dr. Muhammed Al-Abd Al-Aali ya kuma kara da cewa, yawan alhazan da suka fuskanci matsalar tsananin zafin ranar ya wuce dubu shida da dari bakwai.

Dr. Muhammad ya ce Sun shaidawa alhazai cewa kar su dauki kaya zuwa wurin jifa, da zuwa masallacin Ka’aba, sannan su kula da tafiya cikin natsuwa da kauce ma shiga turmutsitsi.

A ranar Arfa alhazai sun rika amfani da laima, yayin da zafin rana ya kai maki 45 a ma’aunin yanayi

Hukumomin Saudiyya dai sun samar da dubban ma’aikatan lafiya domin kula da alhazai a bana, yayin da masu aikin sa kai ke raba ruwan sha.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai