• Home  
  • Rundunar ‘Yan sanda ta musanta batun janye jami’anta daga kare manyan mutane
- Labarai

Rundunar ‘Yan sanda ta musanta batun janye jami’anta daga kare manyan mutane

Hukumar ƴan sandan Najeriya ta musanta labarin da ke cewa ta janye jami’anta waɗanda ke aikin kare wasu tsofaffin jami’an gwamnati.

Rundunar 'Yan sanda ta musanta batun janye jami'anta daga kare manyan mutane

Hukumar ƴan sandan Najeriya ta musanta labarin da ke cewa ta janye jami’anta waɗanda ke aikin kare wasu tsofaffin jami’an gwamnati.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce mutane su yi watsi da sanarwar saboda karya ce tsagwaronta.

Ta ce a sanarwar da aka fitar, an nuna sanya hannun mataimakin kwamishinan yan sanda mai muƙamin DCP, wanda shi kaɗai zai nuna cewa karya ce saboda irin wannan, mataimakin kwamishinan ƴan sanda mai muƙamin ACP ne ya kamata ya sanya hannu.

Muƙaddashin Sifeton Ƴan Sandan na ƙasa, Kayode Adeolu Egbetokun, ya ce za su gudanar da bincike domin gano waɗanda suka fitar da sanarwar domin su fuskanci hukunci.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000