• Home  
  • Ya kamata a yi takatsantsan wajen ba wa Ganduje shugabancin APC ~ Dokta Salihu Lukman
- Labarai

Ya kamata a yi takatsantsan wajen ba wa Ganduje shugabancin APC ~ Dokta Salihu Lukman

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC na ƙasa shiyyar arewa maso yamma  Dokta Salihu Lukman, ya ƙara jaddada cewa take-taken neman ɗora tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje

Ya kamata a yi takatsantsan wajen ba wa Ganduje shugabancin APC ~ Dokta Salihu Lukman

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC na ƙasa shiyyar arewa maso yamma  Dokta Salihu Lukman, ya ƙara jaddada cewa take-taken neman ɗora tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyar na ƙasa, ya saɓa wa dokokin jam’iyar ƙarara.

Haka kuma Dokta Lukman ya bayar da hujjojin cewa akwai fa maganar duba sanin ya kamata da ɗabi’u na gari kafin a ce za a naɗa Ganduje shugaban jam’iyar APC na ƙasa.

Dokta Lukman ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya nisanta kansa da duk wata ƙumbiya-ƙumbiyar neman naɗa Ganduje shugaban jam’iyar APC.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000