Gwamnatin jahar Gombe, ta bayyana cewa za ta mayar da dukkan burtalan da ke cikin jihar karkashin kulawarta.
Gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti da ya kunshi shugabannin manoma da makiyaya da sarakunan gargajiya da masana muhalli da sauran su, domin duba wannan shirin.
Wannan mataki na gwamnatin na da nasaba da irin halin da aka shiga na yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya.
Gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya shaida wa manema labarai cewa wajibi ne a yi maganin wannan matsala ta yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya.