• Home  
  • Ajuri Ngelale ya zama mai ba wa shugaba Tinubu shawara na musamman kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a
- Labarai

Ajuri Ngelale ya zama mai ba wa shugaba Tinubu shawara na musamman kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Ajuri Ngelale a matsayin babban mashawarcinsa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a kuma mai magana da yawunsa.

Shugaba Bola Tinubu ya nada Ajuri Ngelale a matsayin masharcinsa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Ajuri Ngelale a matsayin mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a kuma mai magana da yawunsa.

Kamar yadda wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta nakalto, nadin na Ajuri ya fara aiki ne nan take daga ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata.

Tinubu ya bukaci sabon mai magana da yawun nasa da ya yi amfani da kwarewa da gogewarsa wajen gudanar da aikin da ke gabansa a halin yanzu.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wannan nadin, Ngelale ya ce, ya yi matukar farin ciki da annashuwa bisa zabin da shugaban ya yi masa, tare da shan alwashin zai yi aiki tukuru domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai