A nan ma Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ma’aikatan ƙasar nan alƙawarin cewa nan gaba kaɗan gwamnatinsa za ta ƙara musu albashi, kamar yadda ya bayyana a cikin jawabinsa na yammacin Litinin.
Kazalika ya sake shan alwashin ɓullo da matakan sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa raɗaɗin da suke ji na cire tallafin man fetur, wanda ya ce “wasu mazambata ne ke amfanarsa”.
Tinubu ya ƙara da cewa “A cikin wata biyu, sun adana sama da naira tiriliyan ɗaya na tallafin mai da a da ake kashewa, wanda a da ‘yan sumoga da mazambata ke amfana da shi.
Cikin jawabin da ya gabatar na minti 20 ta kafar talabijin ɗin gwamnatin tarayya, Tinubu ya nemi ‘yan Najeriya da su ƙara haƙuri.
Cikin matakan da gwamnatin ta Tinubu ta ɗauka, akwai ba da umarnin rarraba tan 200,000 na hatsi a faɗin ƙasar don a sayar kan “sassauƙan farashi”.
Sai dai jawabin shugaban bai taɓo batun soke tsauraran sharuɗɗa ba game da dokar bayar da bashin kuɗin karatu, wanda gwamnatinsa ta ba da sanarwa jim kaɗan kafin ya fara jawabin.