DAGA: YASIR ADAMU
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ware duk ranar 29 ga watan Oktoba na kowace shekara a matsayin ranar tunawa da ciwon shanyewar barin jiki.
Taken ranar bana shi ne Together we are Greater Than Stroke wato Mu Haɗu Mu Yaƙi Shanyewar Ɓarin Jiki Tare.
Albarkacin ranar Muhasa Radio ya yi duba na tsanaki game da wannan cuta ta shanyewar barin jiki inda wakilinmu Yasir Adamu ya leka asibitoci kuma ya samu zantawa da masu lalurar shanyewar ɓarin jikin da kuma likitan da ke lura da irin wannan ciwo.
Ya fara ne da farko da ziyartar asibitin ƙwararru na Murtala da ke ƙwaryar birnin Kano inda na yi katarin samun Dokta Aliyu Dausayi wanda ya yi karin haske kan abubuwan da suke jawo wa mutum kamuwa da cutar shanyewar barin jiki.