A yau Talata ake sa ran dawowar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Najeriya
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Tinubu wanda ya bar kasar a ranar 20 ga watan Yuni zuwa birnin Paris na da niyyar komawa Najeriya don yin bukin babbar Sallah a gida.
An shirya cewa Shugaban kasar, zai koma Abuja daga Paris a ranar Asabar da ta gabata, amma daga nan sai ya wuce birnin Landan don gudanar da ziyara ta kashin kansa.