Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Laraba 28 da Alhamis 29 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan babbar Sallah na shekarar 2023.
Bukin sallar Eid Kabir bukin ne da al’ummar musulmi a fadin duniya ke gudanarwa kowace shekara a ranar 10 ga watan Dhul Hijja.
Bukin na da mahimmanci a addinance, kuma musulmai daga birane na kokarin komawa gida domin gudanar da bukuwan sallar tare da ƴan uwa da abokan arziki.
Ana yanka rauguna kamar yadda addinin musulunci ya tanada tare da kuma taruwa a filin idi domin gabatar da sallah da safe.