Yayin da ake ci gaba da lissafa gwamnonin da suke sauya sheƙ zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ya ce yana nan a jamiyyarsa ta PDP daram.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Gwamnan ya musanta hakan ne a wata hira da BBC ta yi da shugaban jam’iyyarsa ta PDP a jihar Bauchi wanda ya yi magana da yawun gwamnan.
Pharmacist Sama’ila Adamu Burga, shugaban jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, ya ce jita-jita ce kawai.
“Da wa aka yi? kuma da wa gwamnan na Bauchi ya yi shawarar sauya shekar? to duk wannan jita-jitace kawai da soki burutsu,” in ji shi.

