Wasu da ake zargin mayaƙan ‘yan Boko Haram sun far wa wani ƙauye a jihar Adamawa, inda suka kashe mutum uku tare da lalata kayayyaki da dama.
Mazauna ƙauyen na Dabna da ke karamar hukumar Hong na jihar ne sun ce mayaƙan sun shigo ƙauyen ne kan babura a safiyar jiya Litinin.
Ya ce sun yi ta harba bindigogi kan mai uwa da wabi tare da sace kayan abinci da kuma magunguna.
Wani jami’in bijilanti ya ce fararen hula huɗu ne suka mutu a harin, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin maharan ya rasa ransa yayin artabu da wasu jami’ansu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje ya fitar, rundunar sun tabbatar da kai harin, inda suka yi Allah-wadai da shi.
Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu sun tura tawaga zuwa yankin domin kwantar da hankula.