Home » Adamawa:INEC Ta Fitar Da Ranar Ƙarasa Zaɓen Gwamna Da Aka Dakatar

Adamawa:INEC Ta Fitar Da Ranar Ƙarasa Zaɓen Gwamna Da Aka Dakatar

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ayyana ranar Laraba 29 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta sake gudanar da zaben kujerar gwamna a wasu akwatinan 39, domin ciki gurbin zaben a Jihar Adamawa.

INEC ta sanar da zaben kujerar gwamna da ta gudanar ranar Asabar a jihar a matsayin bai kammalu ba, domin kuri’un da aka soke sun fi wanda dan takarar da ke kan gaba a zaben ya samu.

INEC Ta ce dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya samu kuri’u 421,524, sai ‘yar takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani ta zo na biyu da kuri’u 390, 275.

Farfesa Muhammad Mele, ya ce hukumar za ta sake zabe a cibiyoyin kada kuri’a 69, da aka soke zabensu, da suke da kuri’u 41,796, da katin zabe dubu 37,016.

Sai dai a wani taron manema labarai, mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar, Felix Tangwami, ya zargi kwamishinan INEC na jihar Barista Hudu Yunusa Ari, da kara yawan cibiyoyin zuwa 77.

Ya kara da cewa ba za Su amince da shi ba, Sun bukaci lauyoyinsu da su dauki mataki, domin bai kamata a maishe su da jiharsu, wajen wasan kwaikwayo ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?