Ƙungiyar kishin ƙabilar yankin Yarabawa da aka fi sani da Afenifere ta ja hankalin shugaban ƙasa Bola Tinubu akan fifita ‘yan ƙabilar Yarabawa wajen ba da muƙamai a ƙunshin gwamnatin sa.
Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da shugaban ƙungiyar Ayo Adebanjo, da kuma sakataren yaɗa labaran ta Justice Falaye suka fitar a jihar Oyo.
Ƙungiyar rajin kare hakkin Yarabawan ta yi gargadin cewa nuna fifikon zai iya kawo barazana ga alaƙar dake tsakanin ƙabilun Najeriya.
- Ana Caccakar Gwamnatin Tunubu Kan Kamen Ƙananan Yara
- Tinubu Ya Lashi Takobi Sai An Ƙara Haraji A Najeriya
Afinifere ta kuma ƙara da cewa akwai buƙatar shugaban ya gyara kuskuren da tace ya yi wajen raba muƙamai.
Sanarwar ta ƙara da cewa baza ta lamunci nuna fifiko ko son rai ba, inda Tinubu ya naɗa shugabannnin hukumomin yaƙi da miyagun laifuka da kuma tattalin arziƙi.
“Baza mu gama yaƙi da abinda muka kira gidan Fulani ba, sannan yanzu mu goyi bayan kaka-gida na Yarabawa ko wata ƙabila.” A cewar ƙungiyar.
Efinifere na daga cikin manyan kungiyoyin ƙabilu mai faɗa aji ta Najeriya, duk da cewa shugaban ƙasar ya fito daga ƙabilar ta Yarabawa ƙungiyar tana Allah wadai da yadda ake rabon muƙamai a gwamnatin.