Home » Ali Madakin Gini Ya Fita Daga Tsarin Kwankwasiyya

Ali Madakin Gini Ya Fita Daga Tsarin Kwankwasiyya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Ɗan Majalisa mai wakiltar Dala a tsakiyar birnin Kano kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya, Ali Sani Madakin Gini ya fita daga tsagin Kwankwasiyya a cikin jam’iyyarsa ta NNPP.

Ali Sani Madakin Gini ya tabbatar da haka ne bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda a ciki aka ji yana cewa “Daga yau, na daina harkar Kwankwasiyya”.

An ji Ali Madakin Gini ya na bayyana cewa “Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce”.

Ɗan Majalisar ya tabbatarwa kafar yaɗa labarai ta BBC cewa: “Na fahimci cewa an gina tafiyar Kwankwasiyya ce kawai domin ci gaban Kwankwaso”.

Kawo yanzu dai ba a ji wani martani daga ɓangaren jagoran tafiyar kwankwasiyyar ba.

Ali Madaki ya ce har yanzu yana nan a jam’iyyarsa ta NNPP, amma ba ya tsagin jagorancin Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Wannan matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano, wanda jam’iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun.

An jiyo Ali Madakin Gini yana yaba wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da cewa shi mutumin kirki don haka ya shawarce shi da ya yi duk yadda zai yi, ya tsaya da ƙafarsa.

A kwanan baya ne dai wata ƙungiya ta ɓullo a fagen siyasar Kano mai taken ‘Abba Tsaya da Ƙafarka’ mai rajin gwamnan na Kano ya daina biyayya ga jagoran Kwankwasiyya, ya ci gashin kansa.

Ana zargin cewa dai wannan lamarin ne ya janyo jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Jihar da wani Kwamishina.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?