Ministan ayyuka a Najeriya, Sanata David Umahi ya ce kamfanin gine-gine na Julius Berger na neman sama da naira triliyan ɗaya domin kammala aikin babban titin Abuja zuwa Kaduna.
Da yake magana a wani taro da daraktocin ma’aikatar ayyuka a Abuja, ministan ya ce farko an ware wa aikin titin Naira miliyan dubu 165 daga bisani aka ƙara kuɗin zuwa naira miliyan dubu 654.
Sai dai ya ce a yanzu gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin da kamfanin ya nema saboda rashin kuɗi.
Majiyarmu ta ruwaito cewa an ba da kwangilar aikin ne tun a shekarar 2017 amma ba a fara ba sai a shekarar 2018, kuma tun shekarar 2021 ya kamata a kammala titin wanda ɗaya ne daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Buhari.
Sai dai hakan bai samu ba har gwamnatin ta sauka a shekarra 2023 duk da cewa rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka an kammala fiye da rabin aikin titin.