Home » Kano: Rundunar ‘yan sanda ta kaddamar da rajistar ababen hawa

Kano: Rundunar ‘yan sanda ta kaddamar da rajistar ababen hawa

by Anas Dansalma
0 comment
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel,  ta bakin kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel,  ta bakin kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya buƙaci al’ummar jihar da su fara yin rajistar ababensu na hawa ta shafukan intanet ɗin da hukumar ta tanada tare da samun takardun shaidar rajistar.

 

Wannan na ƙunshe ne a cikin umarnin da Sufeto Janar na ‘yan sandan ƙasar nan, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, aike wa kwamishinonin ƴan sanda, kuma tuni reshen rajistar ababen hawa a nan Kano ya fara aikinsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel,  ta bakin kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Sannan ga masu neman bayani game da ababen hawa ko sanar da rundunar sauyin mallaka na ababen hawa da sauya launin abin hawa da gangar jikin abin hawan ko canza lamba duk za su iya yi ta shafin da rundunar ta samar.

 

A cewar rundunar ƴan sandan, wannan wani yunƙuri ne na samun bayanai kan ababen hawa domin samun sauƙin gudanar da bincike wajen kawo ƙarshen laifuffukan da suka shafi satar ababen hawa a Najeriya.

 

Wannan rajista ta haɗa da motoci da babura masu ƙafa biyu, da masu ƙafa uku domin tabbatar da tsaro da kare dukiyar al’umma,  rundunar ta kuma buƙaci al’umma su sanar da ita duk wani motsin da ba su gamsu da shi ba a ofishinta mafi kusa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi